FATAWOWIN RAHMA (TAMBAYOYI DA AMSOSHI)
TARE DA: PROF. MUHAMMAD SANI UMAR R/LEMO
FILE: | 002 FATAWOWIN RAHMA.mp3 |
---|---|
SIZE: | 11.93 MB |
Fatawowin Rahma
10 Rajab 1443
12 February 2022
Tare da: Ass. Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo
Shimfiɗa: Watan Rajāb
Tambayoyi da Amsoshin da ke ciki
1. Har yanzu ana iya fassarar mafarki a Musulunci?
2. Diyya (blood-money) da ake biyan sojoji da suka mutu a wajen yaƙi da 'yan ta'adda zai shiga gado ko kuma za a bawa na kusa da mamaci (Sojan), watau next of kin, da shi Sojan ya bayar a matsayin mai karɓar 'diyyar' in ya mutu?
3. Mace ta yi shekara bakwai ba ta tare da mijinta, tana gidansu. Sai ya bata takardar saki, bayan wata ɗaya sai tayi aure. Auren ya yi?
4. Mace za ta iya amfani da sunan mijinta maimakon mahaifinta?
5. Shin yaron da Iyayensa suka ciyar da shi da ribâ ko kuɗin haramun zai shiga cikin faɗin Manzon Rahma ﷺ ' duk tsokar da aka gina da haramun makomarta wuta ce'