YA MUTU YANA SHAN TABA SIGARI
TARE DA: DR. JAMILU ZAREWA

YA MUTU YANA SHAN TABA SIGARI
TAMBAYA:
Assalamu Alaykum, Ina fatan Dr yana Lafiya. Dan Allah mene ne Hukuncin Mai shan taba (sigari), har ya mutu bai tuba ba? Na gode.
AMSA:
Wa'alaikumus salaam wa rahmatullahi wa barakaatuhu, Dukkan wanda ya mutu yana shan taba (sigari) bai tuba ba, yana karkashin ikon Allah, in ya so ya gafarta masa, in ya so ya kama shi da zunubin shan tabar da ya yi, saboda shan taba haramun ne, saboda ta kunshi cuta, kuma duk abin da yake cuta ne tsantsa haramun ne, kamar yadda ayoyin Alqur'ani da hadisan manzon Allah suka tabbatar.
Allah ne mafi sani.
11/05/2016
03/08/1437
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
