HUKUNCIN  SANYA WA JARIRI SUNA HANEEF KO HANEEFA

AMSAWA: JAMILU IBRAHIM SARKI, ZARIA.

HUKUNCIN  SANYA WA JARIRI SUNA HANEEF KO HANEEFA

HUKUNCIN IYAYEN DA SUKE  SANYA WA JARIRI SUNA HANEEF KO HANEEFA

TAMBAYA
Assalamu Alaikum, malam Allah ya qara lafiya, tambayata ita ce sunan yarona Muhammad, amma ana kiran shi Haneef saboda sakaya sunan mahaifina, yanzu kuma ina son in sa ma yarinyata Haneefa a matsayin zanannen suna, dan Allah malam wadannan sunaye sun inganta, Hanif da Hanifa?

AMSA
Wa'alaikumus salam, kalmar Haneef kalma ce mai kyau, wadda take da kyawawan ma'anoni mabambanta. A qamus ɗin Mu'ujamul Waseeɗ an bayyana kalmar Haneef (حنيف) da ma'anar: "mai karkata daga sharri zuwa alheri". Kuma an fassara ta da ma'anar: "ingantacciyar karkata zuwa ga Musulunci, tare da tabbata a kansa".


A qamusun Mu'ujamurrá'id kuma an bayyana kalmar Haneef da: "Wanda ya tsarkake Musuluncinsa ya tabbata a kai". Sannan kuma Allah S.W.T. ya ambaci kalmar a wurare da dama a cikin Alqur'ani, misali a Suratu Áli Imran aya ta 67, da Suratur Rum aya ta 30. Waɗannan kalmomi da ke cikin waɗannan ayoyi duk sun zo ne suna nuna kyawon Musuluncin waɗanda ake magana a kansu.


Waɗannan dalilai ne da suke nuna cewa kalmar Haneef da Haneefa kalmomi ne masu kyau, babu matsala don an sa wa yaro Haneef ko an sa wa yarinya Haneefa.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Nature
  • Inusa abubakar adamu
    Inusa abubakar adamu
    Allah ya kara daukaka da sanin addinin musulunci
    1 year ago Reply  Like (1)