ILLAR DAKE TATTARE DA ZINA

Zina tana jawo masifu da bala'i wanda duk mai hankali idan yayi tunani bai kamata ya kai kansa cikin ta ba koda babu Shari'ar da zata hana yin taba.

ILLAR DAKE TATTARE DA ZINA
ILLAR DAKE TATTARE DA ZINA

Babu abinda mutum yake samu a zina banda taɓewa da nadama da yake biyo baya, zina babu wani alheri dake tare da ita banda ƙasƙan ci da wulakanci da mutum yake tsintar kansa akai tun daga nan duniya kafin aje lahira.

Zina tana jawo masifu da bala'i wanda duk mai hankali idan yayi tunani bai kamata ya kai kansa cikin ta ba koda babu Shari'ar da zata hana yin taba. Illar da zina take jawowa yafi dukkan yadda mutum zayyi tunani. 

Shiyasa cikin hikima da Buwaya irin ta Ubangiji yace kada a kusance tama balle a aikata ta saboda irin illar da take jawowa dan Adam.
 
 Zina tana jawo fushin Ubangiji ya sauka ga bawa komai yaki da dadi, tana jawo tawayar arziki da rashin sanin manufa a rayuwa, tana saka kuncin zuciya da munana zato ga mutane, tana tafiyar da kwarjini da ƙima a idan mutane, illar zina yana shafar har zuria ta kuma jawo musu ƙasƙan ci, tana tafiyar da imani da kunya ga mutum, tana sa mutum ya rayu cikin nadama da wulakanci.

Illar zina munin ta yafi karfin a rubuta su, ku nisan ci zina domin babu wani alheri dake tare da ita. Allah ya tsare mu ya kare mu. Aameen!