KARATUN LITTAFIN ARBA'UNA (40) HADITH
TARE DA: SHEIK JA'AFAR (RAHIMAHULLAH)
TAKAITACCEN TARIHIM MARIGAYI MALAM JA'AFAR
Marigayi Malam Ja'afar Mahmud Adam (an haife shi ne shabiyu (12) gawatan Fabrairu a shekarar 1960. Ya bar duniya 13 gawatan Afrilun shekarar 2007).
Haifaffen garin Daura ne ta jahar Katsina amma ya girma a birnin Kano.Ya rasu ne sanadiyar harbin bindiga da wasu da ba a san ko su waye ba, sun harbe shi a lokacin da yake sallar Asubahi a masallaci a garin Kano a Unguwar Dorayi, Malamin Addinin Musulunci ne, Ahlus-Sunnah ma'ana: mabiyin kungiyar Jama'atu Izalatul Bid'ah Wa Ikamatus Sunnah Izala ne a Najeriya kungiyar Addinin Musulunci da take kokarin Kawar da Bidi'a (wato ibadun da basu da tushe a Musulunci) da tabbatar da Sunnah, wanda babban cibiyan kungiyar ta ke a Abuja.
Bayan haka ya kasance mallamin Tafsirin Al-Kur'ani mai girma. Sannan za'a iya cewa shi ne jagoran salafawa-sunni ta Najeriya.
Allah SWT ya jikan malam da gafara. Aameen!