FATAWOWIN RAHMA (TAMBAYOYI DA AMSOSHI)
TARE DA: PROF. MUHAMMAD SANI UMAR R/LEMO

FILE: | 004 FATAWOWIN RAHMA.mp3 |
---|---|
SIZE: | 12.12 MB |
Fatawoyin Rahma
11 Rajab 1443
13 February 2022
Ass. Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo
Shimfiɗa : Rasa Imani Ya fi Komai Matsala !
Tambayoyi da Amsoshin da ke ciki -
1. Gidan da aike sauraron karatun Suratul Baƙara a MP3 ko TV, ko Wayan hannu Shaiɗanu za su kaurace wa gidan tamkar gidan da Mutum yake karantawa da kansa?
2. Wanda ya sayi carpet ɗin Massalaci zai cigaba da samun lada ko da an canza ‘Carpet’ ɗin saboda tsufa?
3. Za a iya sadaƙa ga mamaci a makwafin bashin da ake binsa?
4. Wanda ya saci kuɗin kafiri ya zai yi ya kuɓuta alhali kafirin ya mutu?
5. Salla a massalaci mai jama'a da yawa ya fi lada a massalaci mai jama'a kaɗan?
6. Ya hallata Mutum ya ƙi fita Sallar Asuba saboda rashin zaman lafiya?
7. Wanda ya karya azumi da gangan zai iya ciyarwa kai tsaye?
8. Ƙa'idar sharia ce dukkan ɗan ƙwai halal ne?
9. Ya inganta faɗin 'Subhannallah Malikil Ƙuddus sau uku bayan Witr?
10. Wajibi ne karanta Bismillah kafin fara karanta Fatiha a Salla?
11. Ya hallata zuwa massalaci nesa saboda limamin yafi kamanta sunna akan massalacin da ya fi kusa?
12. Hukuncin faɗin 'Àmiin' bayan Liman ya gama karanta Fatiha!
13. Ɗalibai da suka kai sha huɗu za su iya yin Sallar Jumu'a a Jami'a?
14. Hukuncin wanda zai bi Liman sallah amma bayan kabbarar Harama sai yayi gum ba ya yin wata kabbara ko wani zikiri!
15. Mutum zai iya yin ima'i domin samun Jam'in farko maimakon ya jira jam'i na biyu a massalacin da ake cika fal?
16. Ka'idace duk wanda ya kira salla shi zai yi iƙama?
17. Hukuncin bin Limamin da ba ya rera Al-ƙur'ani!
18. Ya ya lamarin wanda ko ya yi Azkar amma Shaiɗanu ba sa kyale shi?
19. Shawara ga wanda in ya kwanta a ɓangaren dama ba ya bacci!
