ALLAH YA NA AMSA MA BAWANSA ADDUA SAN DA YA GA DAMA BA LALLAI LOKACIN DA BAWAN YAKE SO BA
TARE DA: ASS. PROF. MUHAMMAD SANI UMAR R/LEMO
FILE: | FATAWOWIN RAHMA.mp3 |
---|---|
SIZE: | 12.12 MB |
Fatawowin Rahma
12 Jumada Akhir 1443
15 January 2022
Tare Da Ass. Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo
Shimfiɗa - Allah ya na amsa ma bawansa addua san da ya ga dama ba lallai lokacin da bawan yake so ba!
Tambayoyi da Amsoshin da ke ciki -
1. Hukuncin tayar da iƙama kafin a ayyana limamin da zai ja sallar?
2. Yana da asali in Mutum ya yi saukar Al-ƙur'ani ko haddar Al-ƙur'ani sai ya yi walima?
3. Dole ne mutum sai yayi wa kansa addua kafin ya yi wa wani?
4. Ya inganta Annabi Ibrahim yana tallan gumakan mahaifinsa?
5. Hukuncin wanda ya tsinci kuɗi ya yi amfani da su saboda mai kuɗin ya yi shelar kuɗin da aka sace sun fi yadda aka tsinta yawa!
6. Wanda ya hau babur yana gudu da ya wuce hankali har ya kashe wani -
yayi kisan ganganci?
7. Ɗan Zina zai yi gado?
8. In Mutum ya yi gyatsa zai ce ' Alhamdulillah'?
9. Ya hallata ma'aikaci ya yi wani aiki a wata ma'aikata idan inda yake aiki ba a fara aiki a wannan lokacin?
10. Hukuncin wanda baya zuwa aiki kullum saboda babu aikin kullum!
11. Mace da ta yi amfani da allurar tsarin iyali sai jinin ta ya wuce al'adarta - yaya zata yi?
12. Hukuncin wanda baya sallah sai ya ga dama