YADDA AKEYIN SUJJADAR QABLI DA SUJJADAR BA’ADI

YADDA AKEYIN SUJJADAR QABLI DA SUJJADAR BA’ADI

YADDA AKEYIN SUJJADAR QABLI DA SUJJADAR BA’ADI
YADDA AKEYIN SUJJADAR QABLI DA SUJJADAR BA’ADI

YADDA AKEYIN SUJJADAR QABLI DA SUJJADAR BA’ADI

TAMBAYA:

Assalamu alaikum.
Barka da dare malam Dan Allah Ina tambaya. Malam maye rafkanuwa? Dakuma Ba'adi? Kabali? Ya akeyinsu sannan wace sallah ce ba ayimata rafkanuwa baadi ko kabali?

AMSA:

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

1. SUJJADA QABLI:

Ana yinta ne kafin sallama. Bayan mutum yayi tahiya, kafin yayi sallama, sai ya sake yin wasu sujjudu guda biyu, sannan ya sake yin wata tahiyar, Sannan yayi sallama. Wannan ita ce Sujjadar Qabaliy, Dalilan da suke sawa ayi ta: Idan mutum yayi ragi a cikin Sallarsa, Ko kuma ya tauye wasu sunnoni Qarfafa guda biyu ko sama da haka. (a takaice kenan).

2. SUJJADA BA’ADI :

Ana yinta ne duk yayin da aka Qara wani abu acikin Sallah. Kokuma yayin da mutum ya mance da wata farillah, ko kuma rukuni daga cikin sallar sa. Bayan ya kawo wannan farillar da ya mance, to sai yayi sujjadar Ba’adi.

YADDA AKE YINTA :
 Ana yinta ne bayan anyi tahiya anyi sallama, sai a sake yin wasu sujjudu guda biyu, sannan ayi tahiya ayi sallama.

ﺑَـﺎﺏٌ ﻓِﻲ ﺍﻟﺴُّﺠُﻮﺩِ ﻗَﺒْﻞَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ
ﻭَﺃَﻣَّﺎ ﺍﻟﺴُّﺠُﻮﺩُ ﺍﻟْﻘَﺒْﻠِﻲُّ ﻓَﺴَﺒْﻌَﺔٌ :
ﻓَﻤَﻦْ ﻧَﺴِﻲَ ﺗَﻜْﺒِﻴﺮَﺗَﻴْﻦِ ﻓَﺄَﻛْﺜَﺮَ ﻏَﻴْﺮَ ﺗَﻜْﺒِﻴﺮَﺓِ ﺍْﻹِﺣْﺮَﺍﻡِ ﺳَﺠَﺪَ ﻗَﺒْﻞَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﻧَﺴِﻲَ ﺳَﻤِﻊَ ﺍﻟﻠﻪُ ﻟِﻤَﻦْ ﺣَﻤِﺪَﻩُ ﻣَﺮَّﺗَﻴْﻦِ ﻓَﺄَﻛْﺜَﺮَ ﺳَﺠَﺪَ ﻗَﺒْﻞَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﻧَﺴِﻲَ ﺍﻟْﺠَﻠْﺴَﺔَ ﺍﻟْﻮُﺳْﻄَﻰ ﺳَﺠَﺪَ ﻗَﺒْﻞَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﻧَﺴِﻲَ ﺍَﻟﺘَّﺸَﻬُّﺪَ ﺳَﺠَﺪَ ﻗَﺒْﻞَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﻧَﻘَﺺَ ﻭَﺯَﺍﺩَ ﺳَﺠَﺪَ ﻗَﺒْﻞَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﺃَﺳَﺮَّ ﻓِﻴﻤَﺎ ﻳُﺠْﻬَﺮُ ﻓِﻴﻪِ ﺳَﺠَﺪَ ﻗَﺒْﻞَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ .
ﺍِﻧْﺘَﻬَﻰ ﺍﻟﺴُّﺠُﻮﺩُ ﺍﻟْﻘَﺒْﻠِﻲُّ .

 BABIN SUJJADA KAFIN SALLAMA
Amma Sujjadar Kabli guda bakwai ce: –

 • Wanda ya manta kabbara biyu ko fiye banda kabbarar harama sai ya yi sujjada kabli.

 • Wanda ya manta (faɗin) Sami’allahu liman hamidahu, sau biyu ko fiye ya yi sujjada kabli.

 • Wanda ya manta zaman (tahiya) tsakiya ya yi sujjada kabli.

 • Wanda ya manta karatun tahiya ya yi sujjada kabli.

 • Wanda ya rage ya qara ya yi sujjada kabli.

 • Wanda ya asirce (karatu) a inda ake bayyana shi ya yi sujjada kabli.

  sujjada kabli sun tuke

ﺑَـﺎﺏٌ ﻓِﻲ ﺍ ﻟﺴُّﺠُﻮﺩِ ﺍﻟْﺒَﻌْﺪِﻱِّ :
ﻭَﺃَﻣَّﺎ ﺍﻟﺴُّﺠُﻮﺩُ ﺍﻟْﺒَﻌْﺪِﻱُّ ﻓَﺴَﺒْﻌَﺔٌ :
ﻭَﻣَﻦْ ﺗَﻜَﻠَّﻢَ ﺳَﺎﻫِﻴًﺎ ﺳَﺠَﺪَ ﺑَﻌْﺪَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﺳَﻠَّﻢَ ﻣِﻦْ ﺭَﻛْﻌَﺘَﻴْﻦِ ﺳَﺠَﺪَ ﺑَﻌْﺪَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﺯَﺍﺩَ ﺭَﻛْﻌَﺔً ﺃَﻭْ ﺭَﻛْﻌَﺘَﻴْﻦِ ﺳَﺠَﺪَ ﺑَﻌْﺪَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﺍِﺳْﺘَﻨْﻜَﺤَﻪُ ﺍﻟﺸَّﻚُّ ﺳَﺠَﺪَ ﺑَﻌْﺪَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﺟَﻬَﺮَ ﻓِﻴﻤَﺎ ﻳُﺴَﺮُّ ﻓِﻴﻪِ ﺳَﺠَﺪَ ﺑَﻌْﺪَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﺟَﻠَﺲَ ﻓِﻲ ﺍﻟﺮَّﻛْﻌَﺔِ ﺍْﻷُﻭﻟَﻰ ﺳَﺠَﺪَ ﺑَﻌْﺪَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ .
ﺍِﻧْﺘَﻬَﻰ ﺍﻟﺴُّﺠُﻮﺩُ ﺍﻟْﺒَﻌْﺪِﻱُّ .

 BABIN SUJJADA BAYAN SALLAMA
Amma sujjada bayan sallama guda bakwai ce: –

 • Wanda ya yi zance da mantuwa ya yi sujjada ba’adi.

 • Wanda ya yi sallama a raka’a ta biyu yayi sujjada ba’adi.

 • Wanda ya kara raka’a ɗaya ko biyu ya yi sujjada ba’adi.

 • Wanda kokwanto ya aure shi ya yi sujjada ba’adi.

 • Wanda ya bayyana (karatu) a inda ake boyewa ya yi Sujjada ba’adi.

 • Wanda ya zauna a raka’a ta farko ya yi sujjada ba’adi.

  Sujjada ba’adi sun tuke.

ﺑَـﺎﺏٌ ﻓِﻲ ﺍﻟﺴَّﻬْﻮِ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻻَ ﺳُﺠُﻮﺩَ ﻓِﻴﻪِ .
ﻭَﻣَﻦْ ﺗَﺮَﻛَﻬَﺎ ﻓَﺼَﻼَﺗُﻪُ ﺗَﺎﻣَّﺔٌ ِﻷَﻧَّﻬَﺎ ﺳُﻨَّﺔٌ ﻏَﻴْﺮُ ﻣُﺆَﻛَّﺪَﺓٍ
ﻭَﻣَﻦْ ﻧَﺴِﻲَ ﺗَﻜْﺒِﻴﺮَﺓً ﻭَﺍﺣِﺪَﺓً ﻣِﻦْ ﻏَﻴْﺮِ ﺗَﻜْﺒِﻴﺮَﺓِ ﺍْﻹِﺣْﺮَﺍﻡِ، ﺃَﻭْ ﺳَﻤِﻊَ ﺍﻟﻠﻪُ ﻟِﻤَﻦْ ﺣَﻤِﺪَﻩُ ﻣَﺮَّﺓً ﻭَﺍﺣِﺪَﺓً، ﺃَﻭِ ﺍﻟْﻘُﻨُﻮﺕَ، ﺃَﻭْ ﺭَﻓْﻊَ ﺍﻟْﻴَﺪَﻳْﻦِ ﻋِﻨْﺪَ ﺍْﻹِﺣْﺮَﺍﻡِ، ﺃَﻭِ ﺍﻟﺘَّﻴَﺎﻣِﻴﻦَ . ﺃَﻭِ ﺍﻟﺘَّﺴْﺒِﻴﺢَ ﻓِﻲ ﺍﻟﺮُّﻛُﻮﻉِ، ﺃَﻭِ ﺍﻟﺪُّﻋَﺎﺀَ ﻓِﻲ ﺍﻟﺴُّﺠُﻮﺩِ، ﺃَﻭِ ﺍَﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺭَﺑَّﻨَﺎ ﻭَﻟَﻚَ ﺍﻟْﺤَﻤْﺪُ ﻓَﻼَ ﺷَﻲْﺀَ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻓِﻲ ﺟَﻤِﻴﻊِ ﺫَﻟِﻚَ ِﻷَﻧَّﻬَﺎ ﺳُﻨَّﺔٌ ﻻَ ﻳُﺴْﺠَﺪُ ﻟَﻬَﺎ، ﻭَﺇِﻥْ ﺳَﺠَﺪَ ﻟَﻬَﺎ ﺑَﻄَﻠَﺖْ ﺻَﻼَﺗُﻪُ .
ﺍِﻧْﺘَﻬَﻰ ﺍﻟﺴَّﻬْﻮُ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻻَ ﺳُﺠُﻮﺩَ ﻟَﻪُ .

 BABIN RAFKANUWAR DA BA A YI MATA SUJJADA 
WANDA YA BAR TA SALLAR SA TA CIKA DOMIN ITA SUNNA CE BA MAI KARFI BA
Wanda ya manta kabbara guda biyu banda kabbarar harama ko (faɗin) sami’allahu liman hamidahu sau daya tak, ko Alkunutu, ko daga hannaye lokacin kabbarar harama ko damaitawa ko yin tasbihi a ruku’u ko yin addu’a a sujjada ko (fadin) Allahumma Rabbana walakal hamdu, babu komai a gare shi a cikin dukkan wadannan domin su sunnoni ne wadanda ba a yi musu sujjada, idan kuma (mutum) ya yi musu sujjada

 • Muhammad Ibrahim
  Muhammad Ibrahim
  Ubangiji Allah isa mudashe ameen Ubangiji Allah ibiyaka da kyakkewan sakamako
  9 days ago Reply  Like (1)
 • shattiman kanoma
  shattiman kanoma
  Masha allah allah yasaka da alkhairi yakara ilimi mai albarka ameen
  16 days ago Reply  Like (0)
 • Aminu Muhammad Chamalwa
  Aminu Muhammad Chamalwa
  Masha Allah. Na gode da wayan nan bayanen. Jaza Kallahu Khair.
  19 days ago Reply  Like (0)
 • Usman Alh Ahmadu
  Usman Alh Ahmadu
  Masha Allah munagodiya Allah yaqara ilimi
  21 days ago Reply  Like (0)
 • abubakar dahiru
  abubakar dahiru
  allah y sakada alkairi munjidadin wannan bayanin allah y qara ilimi
  3 months ago Reply  Like (8)