HUKUNCIN GINA BANDAKI YANA FUSKANTAR AL-QIBLA

Hadisi ya inganta daga Abu Ayubal Ansari (RA) a cikin  Sahih al-Bukhari da Muslim

HUKUNCIN GINA BANDAKI YANA FUSKANTAR AL-QIBLA

HUKUNCIN GINA BANDAKI YANA FUSKANTAR AL-QIBLA

TAMBAYA
Assalamu alaikum malam mutunne yagina sabon gida saida akagama aikin komai sai yalura ansa toilet yana kallon gabas saiyace acire ajuya a musulunce babu kyau Asa gado ko toilet suna kallon gabas dan Allah malam menene hukuncin haka nagode

AMSA
Wa'alaykumussalam.
Hadisi ya inganta daga Abu Ayubal Ansari (RA) a cikin  Sahih al-Bukhari da Muslim cewa manzon Allah ﷺ ya hana a kalli alqibla ko a bata baya wajen biyan bukata.

Amma jamhurun malamai cikin su akwai Imam malik, Shafi'i da Ahmad Bin Hambal sunce wannan hanin ya shafi wanda zai biya bukatar sa ne a fili inda babu wani shamaki tsakanin sa da alqibla, amma idan akwai shamaki ko cikin irin bayukan mu toh babu komai.

Sauran Malaman kamar su Imam Abu hanifah sunce hanin ya shafi fili da kuma cikin bayi, wannan shine ra'ayin shehul Islam Ibn Taymiyya, (Aduba Al'Mugny 1\107).

An tambayi malaman lajna sun bada fatawar babu laifi idan har akwai shamaki wato wani gini ko makamancin sa aduba Fatawa lajna 5\97.

Don haka idan har ka riga ka gina bayin toh babu komai akan ka ba sai ka rusa ba, in kuma kafin ka gina ne to zaka iya gyara tsarin ta yadda zaka kaucewa kallon ka'aba don gujewa duk wata shubuha.
Amma tunda kace ka gyara shikenan muna fatar Allah ya baka ladar nesantar hanin manzon Allah ﷺ.

Zancen saka gado ya kalli gabas ban san wani dalili daya hana haka ba, abinda na sani shine a kwanta a gefen dama kafin ayi bacci a kuma kaucewa kifa ciki.

WALLAHU A'ALAM.

Nature