WURAREN DA KARYA TA HALATTA A MUSULUNCI

Karya dai haramun ne ga musulmi, kuma wajibe ne ya kaurace mata a ko wane irin hali. Karya don gyaran al’umma, aure ko kwato hakki babu laifi a cikinta, hasilima makaryacin da duk wanda ya taimakama karyar yana da lada. Hadisi ya inganta daga Bukhari da Muslim, Ummu Kulsum (R.A) ta ce: Annabi Salallahu Alaihi Wasallama ya ce: mai sulhunta. mutane ba makaryaci ba ne: yana fadin alhairi kuma yana burin alhairi.

WURAREN DA KARYA TA HALATTA A MUSULUNCI

TAMBAYA:

Assalamau alaikum warahamatullah. Malam tambaya nake da ita a musulunci akwai inda karya ta halatta?

AMSA:

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Karya dai haramun ne ga musulmi, kuma wajibe ne ya kaurace mata a ko wane irin hali. Karya don gyaran al’umma, aure ko kwato hakki babu laifi a cikinta, hasilima makaryacin da duk wanda ya taimakama karyar yana da lada. Hadisi ya inganta daga Bukhari da Muslim, Ummu Kulsum (R.A) ta ce: Annabi Salallahu Alaihi Wasallama ya ce: mai sulhunta. mutane ba makaryaci ba ne: yana fadin alhairi kuma yana burin alhairi.

Ummu Kulsum (R.A) ta kara da cewa banji Annabi SAW yana sauki da yin karya ba a cikin maganganun mutane, sai dai cikin abu Uku: yaki, sulhunta mutane, da zancen mata da miji.

WURAREN DA KARYA TA HALATTA

Koda yake Karya haramun ne a asalinta, amma tana iya halatta harma da zamo wajibi mutun yayi karyar. Lura da wannan tambaya, karya ta halatta a gurare kamar haka:

1) Karya ta halatta a lokacin yaki domin razana da tsorata abokan gaba.
2) Karya ta halatta don sulhunta musulmai da dai-daita tsakanin su.
3) Karya ta halatta don inganta rayuwar ma’aurata.
4) Karya ta halatta domin kwato hakkin mai rauni.
5) Karya ta halatta domin kare fitina da barna a bayan kasa.

SHARUDDAN HALATTA KARYA

Lalle karya laifi ce cikin manyan laifuka (Kaba’ir), kuma Allah baya yafe laifin karya sai dai tuba ta gaskiya. Karya na kai mai yin ta  zuwa ga fajirci, shi kuma fajirci na kai mutum zuwa wuta. Makaryaci ba zai gushe ba yana karya har sai an rubuta shi a matsayin makaryaci a gurin Allah. Don haka musulmi ya kiyayi karya a rayuwar sa.

Karyar da ta halatta wanda mai ita kan iya samun lada, sai ta cika sharudda kamar haka:

1) Sai lamarin ya kasanci babu mafita a cikin sa idan bakaryar aka yiba.
2) Manufan karyar ya kasance maslaha ne kuma alhairi ne kuma babu cutarwa.
3) Kuma a tuba daga baya a nemi gafarar Allah.

Allah muke roko ya gafarta mana baki daya.

Nature